Pochettino bai damu da yawan jan kati da na gargadi da ake bai wa ‘yan Chelsea ba

Maurico Pochettino bai yadda cewar rashin da’ar ‘yan wasa ce ta kai Chelsea ba ta kokari a Premier League ba, wadda ke kan gaba a karbar katin gargadi da yawa a bana.

Chelsea ta karbi kati mai ruwan dorawa biyar a wasan da Wolverhampton ta doke ta 2-1 a Molineux ranar daya kafin Kirsimeti.

Cikin ‘yan wasan sun hada da Christmas Eve da Cole Palmer, wand aba zai yi Chelsea da Crystal Palace ba ranar Laraba, sakamakon katin gargadi biyar da aka bashi.

Haka shima Raheem Sterling ya karbi katin gargadi daf da za a tashi daga wasan.

Tun farko an bai ‘Yan wasan Chelsea jan kati da suka hada da Reece James da Malo Gusto da kuma Conor Gallagher.

Saura kati mai ruwan dorawa daya da idan aka bai wa Nicolas Jackson zai cika 10 a bana, wanda zai yi hutun wasa biyu, wanda aka dakatar a cikin Satumba bayan da ya karbi biyar.

Pochettino ya kara cewar aikin da yake gabansa kara bunkasa wasannin kungiya, ya kara da cewar yanayin wasannin gasar ne ke sawa ‘yan wasan ke nuna damuwarsu.

Kociyan ya yi nuni da cewar ‘yan wasan kungiyar da yawa da ke jinya ne ke kawo musu koma baya a kakar nan.

Enzo Fernandez zai yi jinya a karo na biyu ya yin da har yanzu Pochettino ke cewa Christopher Nkunku da Romeo Lavia ba su murmure ba da a za fara wasa da su ba.

Leave a comment