A jiya Kano Pillars ta doke Enyimba da ci 1-0 a wasan mako na takwas a gasar Firimiya ta Nigeria da suka kara a Sitadiya ta Kofar Mota.
Da wannan sakamakon Kano Pillars mai maki 12 ta koma ta takwas a teburin Firimiyar Najeriya, ita kuwa Enyimba tana ta bakwai mai maki bakwai da kwantan wasa uku.
Sauran sakamakon wasannin mako na takwas ranar Lahadi:
Kwara United 2-2 Shooting Stars
Sunshine Stars 2-2 Rangers International
Katsina United 1-0 Rivers United
Lobi Stars 1-0 Sporting Lagos
Niger Tornadoes 0-0 Bendel Insurance
Kano Pillars 1-0 Enyimba
Remo Stars 4-0 Gombe United
Plateau United 3-1 Abia Warriors