Paris 2024 Olympics: ‘Yan wasan Russia da Belarus sun samu izini

Yan wasan Rasha da Belarus wadanda suka cancanci shiga gasar Olympics ta Paris 2024 za a ba su damar shiga a matsayin tsaka-tsaki (Neutral), amma da Sharudda. In ji kwamitin Olympics na kasa da kasa.

Sharuɗɗan shigar su sun hada da yin wasa ba tare da tutocin kasar su ba, alamumi kasar, da kuma wakokin kasarsu ba.

An dakatar da ‘yan wasa daga wadannan kasashe bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine a watan Fabrairun 2022.

Hukuncin ya zo ne bayan da kungiyoyin wasannin Olympic suka nemi a ba wa ‘yan wasan Rasha da Belarus damar shiga gasar a birnin Paris.

Leave a comment