Osimhen ya tsawaita kwanitaginsa da Napoli zuwa 2026

Victor Osimhen ya tsawaita yarjejeniyarsa da Napoli kan ci gaba da taka leda zuwa karshen kakar 2026.

Kungiyar da ke buga Serie A ce ta sanar da hakan ranar Asabar, sai bai ba ta fayyace kunshin kwantiragin ba.

Amma wasu rahotanni daga Italy na cewa Napoli ta gindaya dalar Amurka miliyan 143 ga duk kungiyar da ke son sayen dan kwallon, idan yarjejeniyarsa bai cika ba.

Ta kuma yi haka ne domin ta kori tarin kungoyin Premier League da ke son zawarcin dan wasan Super Eagles.

Tun farko kwantiraginsa a Napoli zai karkare ne a karshen kakar 2025, bayan da aka yi ta rade-radin makomarsa a kungiyar kan fara kakar nan.

Ya ci kwallo 26 a bara da ya bai wa Napoli damar lashe Serie A, sama da shekara 33 rabonta da kofin tun bayan wanda Diego Maradona ya daukar mata.

Jimilla Osimhen ya zura kwallo 67 a raga a wasa 118, tun bayan da ya koma kungiyar daga Lille a 2020.

A kakar nan Napoli tana da tazarar maki 14 tsakaninta da Inter Milan ta daya a teburin kakar bana.

Kungiyar Frosinone ta fitar da Napoli a Italian Cup a tsakiyar mako.

Leave a comment