Osimhen da Oshoala sune fitattun ‘yan kwallon Afirka

Dan wasan tawagar Nigeria da Napoli, Victor Osimhen ya zama gwarzon dan kwallon kafar Afirka na 2023.

Ya lashe kyautar a wani kasaitaccen biki da aka yi ranar Litinin a Marrakesh a Morocco.

Osimhen, wanda ya lashe Serie A kakar bara da kai wa daf da na kusa da na karshe a Champions League ya yi takara da dan wasan Masar da Liverpool, Mohammed Salah da na Morocco da Paris St Germain, Achraf Hakimi.

Mai shekara 24 ya ci kwallo 26 a wasa 32, wanda ya ja ragamar Napoli ta lashe Serie A karon farko bayan shekara 33.

Tsohon dan wasan Wolfsburg da Lille shi ne ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Italy a farkon shekarar nan.

Osimhen ya ja ragamar Super Eagles da ci mata kwallayen da suka kaita gurbin shiga gasar kofin Afirka da za a yi a Ivory Coast a 2024.

Shi ne na farko da ya shiga cikin ‘yan 10 farko a Ballon d’Or da aka yi a bana, kyautar da Lionel Messi ya lashe.

Ita kuwa Asisat Oshoala ta lashe kyautar karo shida jimilla kenan.

Ta kuma yi takara da ‘yar kasar Afirka ta Kudu da Racing Louisville, Thembi Kgatlana da ta Zambia da Shanghai Sengli, Barbra Banda.

Wadanda suka lashe kyautuka:

Player of the Year (men): Victor Osimhen (Napoli & Nigeria)

Player of the Year (women): Asisat Oshoala (Barcelona & Nigeria)

Coach of the Year (men): Walid Regragui (Morocco)

Coach of the Year (women): Desiree Ellis (South Africa)

National Team of the Year (men): Morocco

National Team of the Year (women): Nigeria

Goalkeeper of the Year (men): Yassine Bounou (Al Hilal & Morocco)

Goalkeeper of the Year (women): Chiamaka Nnadozie (Paris FC & Nigeria)

Young Player of the Year (women): Nesryne El Chad (Lille & Morocco)

Young Player of the Year (men): Lamine Camara (Metz & Senegal)

Club of the Year (women): Mamelodi Sundowns (South Africa)

Club of the Year (men): Al Ahly (Egypt)

Interclub Player of the Year (women): Fatima Tagnaout (AS FAR & Morocco)

Interclub Player of the Year (men): Percy Tau (Al Ahly & South Africa)

Leave a comment