Olympic kwallon mata: Super Falcons za ta kara da South Africa

Tawagar kwallon kafa ta mata ta Nigeria za ta fafata da ta South Africa ranar Juma’a a Abuja, domin neman gurbin shiga gasar Olympic a bana.

Wannan shi ne zagayen farko da za su kece raini a katafaren filin wasa na MKO Abiola, daga baya Afrika ta Kudu ta karbi bakuncin fafatawa ta biyu.

Super Falcons mai kofin nahiyar Afrika tara za ta kece raini da mai rike da kofin da misalin karfe biyar agogon Nigeria, wasa na biyu za a yi a makon gobe ranar Talata a Pretoria’s Loftus Versfeld arena a South Africa.

Rabonda Nigeria ta je kwallon kafar mata a Olympic tun 2008, inda Falcons ta yi rashin nasara a dukkan wasa ukun da ta yi a cikin rukuni a gasar da China ta karbi bakunci.

Nigeria ta taka rawar gani a gasar cin kofin duniya a Australia da New Zealand wata takwas da ya wuce, wadda England ta fitar da ita a bugun fenariti a zagayen ‘yan 16.

Tun a ranar Lahadi tawagar Banyana Banyana ta sauka a Nigeria.

‘Yan wasan Super Falcons da ke sansanin horo

Masu tsaron raga: Chiamaka Nnadozie, Tochukwu Oluehi, Linda Jiwuaku

Masu tsaron baya: Jumoke Alani, Osinachi Ohale, Chidinma Okeke, Shukurat Oladipo, Michelle Alozie, Nicole Payne

Masu buga tsakiya: Rasheedat Ajibade, Toni Payne, Deborah Abiodun, Jennifer Echegini, Christy Ucheibe, Halimatu Ayinde

Masu cin kwallaye: Uchenna Kanu, Gift Monday, Omorinsola Babajide, Ifeoma Onumonu, Esther Okoronkwo, Chiwendu Ihezuo

Leave a comment