Olympiacos za ta kara da Fiorentina a gida a Conference League

Olympiacos za ta buga wasan karshe a filinta a Conference League da Fiorentina bayan da ta ci Aston Villa 2-0 ranar Alhamis.

Kenan ta kai zagayen gaba da cin kwallo 6-2 gida da waje, karon farko da za su yi fatan daukarwa Greece kofin farko a babbar gasar zakarun Turai a tarihi, lokacin da za ta fafata da Fiorentina a Athens ranar 29 ga watan Mayu.

Wannan shi ne karo na biyu da Fiorentina ta kai wasan karshe a Conference League a jere, bayan da ta doke Club Brugge 4-3 gida da waje ranar Laraba.

Tun a 2010 Olympiakos ta yi ta kokarin taka irin wannan matakin karkashin Evangelos Marinakis, amma haka aka dunga fitar da ko dai a zagaye cikin rukuni ko kuma a na ‘yan 16.

Leave a comment