Oklahoma City ta doke Golden State a NBA

Golden State Warriors ta yi rashin nasara ta biyar ranar Alhamis, bayan da Oklahoma City Thunder ta caskara ta.

Thunder ta yi wannan namijin kokarin duk da Stephen Curry da Draymond Green ba su buga mata wasan ba.

Shai Gilgeous-Alexander ya ci maki 24 da ya bai wa Thunder damar shiga gaba, sai Joe mai maki 23 da ‘yan wasan Thunder shida da kowanne ya hada maki masu yawa da suka lashe wasan da cin 128-109.

Ita kuwa Warriros tana da ‘yan wasa bakwai da suka ci mata maki mai yawa da kuma Jonathan Kuminga mai 21.

Fitatcen dan wasan Warriors, Curry na jinya, yayin da Green ke hukuncin dakatarwa wasa biyar, yanzu ya yi daya.

Oklahoma ce kan gaba a zangon farko da tazarar maki 15 a zango na hudu kuwa an bai wa Warriors tazarar maki tara.

Leave a comment