Ƙungiyar Arsenal ta sanar da yin watsi da batun da ake cewar Martin Odegard zai bar Emirates a karshen kakar nan.

Ɗan wasan tawagar Norway ya koma Gunners a Janairun 2021 da fara buga wasannin aro daga baya ta mallake sh.

Kawo yanzu ɗan wasan mai shekara 27 ya buga wa Arsenal wasa 22 da cin ƙwallo 42 da bayar da 45 aka zura a raga.

To sai dai kuma tun daga kakar bara, ɗan wasan na fuskantar kalubale na rashin komawa kan ganiya, bayan jinya da ya sha fama, wanda bai yi karawa 33 ba a dukkan fafatawa.

Arsenal tana matakin farko a kan teburin Premier League ta kuma je ta tashi 1-1 a gidan Bayern Leverkusen a Champions League wasan farko zagaye na biyu ranar Laraba.

Scroll to Top