Hukumar gudanar da gasar Premier ta Najeriya, NPFL ta amince da bukatar Kwara United na zaɓar filin wasa na Mobolaji Johnson a Onikan a Legas.
Tun farko an hukunta Kwara United da mayar da ita buga wasannin gida a MKO Abiola a Abeokuta, sakamakon rikicin da ya ɓarke a wasan mako na 23 a fafatawa da Rivers United.
Kwara United ta ce ta zaɓi komawa buga wasanninta na gida a Legas, domin za ta iya fuskantar adawa daga magoya bayan Remo Stars ta garin Ogun, wadda take ta biyun karshen teburi.
Kwara United tana ta 18 a kasan teburi, shi ya sa ta koma Legas da wasanni, sakamakon da Remo tana mawuyacin hali, kenan kada a samu matsala daga magoya bayanta.
Ranar Lahadi 15 ga watan Maris Kwara United ta fara wasa da tashi 0-0 da Enugu Rangers a Mobolaji.