Djokovic: Nadal na iya zama barazana a Australian open

Dan wasan tennis na daya a duniya Novak Djokovic yayi asashan Rafael Nadal zai iya bada mamaki a gasar Australian Open da za’ayi a watan Janairu 2024, duk da raunin da ya samu.

A koyaushe ina sa ran shi [Nadal] zai taka rawar gani sosai, a gaskiya,” in ji Djokovic, mai shekaru 36, wanda ya lashe Grand Slams uku a 2023.

Ba irin dan wasa bane da zai dawo yawon shakatawa kawai don yin wasa – bari mu ce – a matsakaicin matakin. “Yana son lashe kofuna, Na tabbata cewa horon da shirye-shiryen da yake yanayi ne da niyyar lashe Grand Slam.

Wasansa [Nadal] na karshe yayi rashin nasara a zagaye na biyu akan Mackenzie McDonald na Amurka a gasar Australian Open a watan Janairu 2023.

Leave a comment