NLO 2024: Tudun Wada United ta raba maki da Ahzuba

Tudun Wada United ta kammala wasan cikin rukuni da tashi 1-1 da Ahzuba a gasar Nationwide League Division One ranar Talata.

Wasan da suka buga a Daura jihar Katsina da tsakar rana, Tudun Wada ce ta fara cin kwallo ta hannun Rabi’u Abdullahi da ake kira Rabi’u Pele.

Daga baya ne Ahzuba ta farke da hakan ta kai sun raba maki a wasan karshe a NLO 2024 shiyyar Dura a jihar Katsina.

Sauran sakamakon wasannin da aka kara ranar Talata a Daura Bib FC ta doke CP Boys 2-0, FC Mumbayya 3-0 Arewa, Famous Spiders 2-5 Katsina Junior.

Bayan da aka kammala wasannin cikin rukuni da kowacce kungiya ta buga wada takwas-takwas, Junior Danburan ce ta daya da maki 21, sai Bib ta biyu da maki 16 da kuma Katsina Junior mai maki 14 a mataki na uku.

Tudun Wada United mai maki 13 tana ta hudun teburi, bayan cin wasa uku da canjaras hudu aka doke ta wasa daya.

Leave a comment