NLO 2024: Tudun Wada United ta doke Famous Spiders

Tudun Wada United ta yi nasarar cin Famours Spiders 3-1 a wasa na biyu a cikin rukuni a gasar Nigeria Nationwide League One ranar Litinin.

Tudun Wada United wadda ta lashe Nigeria Amateur League Division Two a bara ta fara cin kwallo ta hannun Rabi’u Abdullahi Pele, kuma shi ne ya kara na biyu.

Daga baya Famous Spiders ta zare daya ta hannun Auwalu Shuaibu, haka suka je hutu Tudun Wada United na cin 2-1.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Tudun Wada United ta kara na uku ta hannun Salisu Abubakar, hakan ya bai wa kungiyar maki ukun da take bukata.

Ranar Asabar Tudun Wada United ta tashi 1-1 da Mumbayya FC a wasan farko a cikin rukuni a wasannin da ake yi a shiyyar Daura jihar Katsina, Nigeria.

Ranar Laraba ne Tudun Wada United za ta buga wasa na uku a cikin rukuni da Junior Danburan.

Kawo yanzu Tudun Wada United ta hada maki hudu a wasa biyu da cin kwallo hudu, yayin da biyu suka shiga ragarta.

Kungiyoyin da ke Daura sun hada da Tudun Wada United da Munbayya FC da Famous Spiders da Junior Danburan da Azuba Boys da CP Boys da kuma Katsina Junior – inda ake sa ran guda biyu ne za su kai zagayen gaba.

Leave a comment