Nkunku ba zai je wasan Newcastle ba – Pochettino

Mauricio Pochettino ya ce Christopher Nkunku ba zai buga wasan da Chelsea za ta ziyarci Nwcastle ba.

Ranar Asabar Newcastle United za ta karbi bakuncin Chelsea a wasan mako na 13 a Premier League.

Dan wasan da Chelsea ta dauka kan fara kakar nan kan fam miliyan 52 daga RB Leipzig ya ji rauni tun kan fara kakar nan.

Chelsea ta yi fama da kamfar cin kwallaye lokacin da dan wasan tawagar Faransa ke jinya.

Sai dai yanzu kungiyar na komawa kan ganiya, wadda ta ci kwallo hurhudu a wasa da Burnley da Tottenham da kuma Manchester City a Premier.

Rabonda kungiyar Stamford Bridge ta ci kwallo hudu tun cikin Afirilun 2022.

Pochettino ya tabbatar da cewar Romeo Lavia, wanda ta dauka daga Southampton kan fam miliyan 53 na daf da warkewa.

Wesley Fofana ya fara atisaye a kokarin da yake na murmurewa, bayan jinya da ya sha.

Chelsea na komawa kan ganiya tun kan a je wasannin kasa da kasa, wadda ta ci wasa biyar daga takwas a dukkan fafatawa.

Haka kuma ta ci kwallo 19, wadda ta zura bakwai a farkon karawa bakwai a baya karkashin Pochettino.

Leave a comment