Super Eagles ta tashi 1-1 da Lesotho a uyo

Super Eagles da Lesotho sun tashi 1-1 ranar Aalhamis a wasan farko a cikin rukuni, domin neman shiga gasar kofin duniya da za a yi a 2026.

Kungiyoyin biyun sun je hutu ba ci, bayan da suka koma zagaye na biyu ne Lesotho ta fara zura kwallo a raga ta hannun Motlomelo Mkhwanazi, daga baya Najeriya ta faeke ta hannun Semi Ajayi.

Super Eagles ta buga karawar ba tare da Victor Osimhen da Samuel Chukwueze da kuma Wilfred Ndidi ba, wadanda ke jinya.

Ranar Laraba Rwanda da Zimbabwe sun tashi 0-0 a wani wasan cikin rukuni na uku.

A rukuni na ukun da ya hada da Najeriya, sauran sun hada da Afirka ta Kudu da Benin da Rwanda da kuma Lesotho.

Za a buga gasar cin kofin duniya a 2026 a Canada da Mexico da kuma Amurka.

Nageriya, wadda za ta buga gasar kofin Afirka a Ivory Coast a badi, ba ta samu zuwa gasar kofin duniya ba a Qatar a 2022.

Super Eagles ta fara halartar gasar kofin duniya a 1996, kawo yanzu ta je karo shida, wadda ta kasa zuwa gasar 2006 da kuma 2022.

Leave a comment