Nigeria ta tashi 1-1 da zimbabwe

Najeriya ta tashi 1-1 da Zimbabwe a wasan neman shiga gasar kofin duniya da suka kara a Rwanda ranar Lahadi.

Tun kan hutu aka ci Super Eagles ta hannun Walter Musona, bayan da suka koma zagaye na biyu ne Najeriya ta ta farke ta hannun Kelechi Iheanacho.

Ranar Laraba Zimbabwe ta tashi ba ci da Rwanda, yayin da Super Eagles ta yi 1-1 da Lesotho ranar Alhamis.

Nageriya da Zimbabwe, wadanda ke rukuni na uku sun buga wasa na bibiyu domin neman gurbin shiga gasar da Amurka da Mexico da Canada za su karbi bakunci a 2026.

Super Eagles, wadda ba ta je gasar kofin duniya ba da aka yi a Qatar a 2022, za ta karbi bakuncin Afirka ta Kudu a cikin watan Yunin 2024.

1 Comment

  • Posted November 19, 2023 6:57 pm 0Likes
    by Abubakar Adamu Danjuma

    Wasa bai mana kyau ba

Leave a comment