Newcastle ta kara cin Man United karo na biyu a bana

Newcastle United ta ci Manchester United 1-0 a wasan mako na 14 a Premier League ranar Asabar a St James Park.

Newcastle United ta ci kwallon a minti na 10 da komawa zagaye na biyu ta hannun Anthony Gordon.

Kenan Godon yana da hannu a cin kwallo bakwai a wasa takwas da cin kwallo biyar ya bayar da biyu aka zura a raga.

Manchester United ta kasa cin Newcastle a wasa hudu kenan a St James Park, inda aka doke ta biyu da canajaras biyu.

Newcastle ce ta fitar da Manchester United mai rike da Caraboa Cup da ci 3-0 a Old Trafford ranar Laraba 1 ga watan Nuwamba.

Manchester United ta kasa cin wasan Premier League a waje da kungiyar da take ‘yan takwas din teburi.

Rabonta da nasara a hakan tun Oktoban 2021 da ta ci Tottenham karkashin Ole Gunner Solskjaer, wadda ta yi canjaras uku aka doke ta 10 daga 13 da ta buga.

Da wannan sakamakon Newcastle ta koma ta biyar din teburin Premier League da maki 26, iri daya da na Tottenham ta shida.

Manchester United ta koma ta bakwai da maki 24, bayan wasan mako na 14.

Ranar Lahadi za a kammala wasannin mako na 14:

  • Chelsea da Brighton
  • Liverpool da Fulham       
  • West Ham United da Crystal Palace       
  • Bournemouth da Aston Villa  
  • Manchester City da Tottenham

Leave a comment