Neuer ne zai tsare ragar jamus a euro 2024

Kociyan Jamus, Julian Nagelsmann ne zai tsare ragar tawagar kasar a gasar cin kofin nahiyar Turai a bana, duk da cewar dan wasan Bayern Munich ba zai buga wasan sada zumunta biyu ba.

Jamus, wadda za ta karbi bakuncin Euro 2024 daga watan Yuni, za ta buga wasan sada zumunta da France da kuma Netherlands.

Tun farko an sa ran mai shekara 37 zai koma buga wa Jamus tamaula a karon farko a Lyon, wanda ya ji rauni tun bayan gasar kofin duniya a 2022 a Qatar, haka kuma ba zai yi wasa da Netherlands ba ranar Talata.

Kenan dan wasan Barcelona, Marc-André ter Stegen shi ne zai tsare ragar Jamus a wasan sada zumunta a Groupama a Lyon da wanda za a yi a Frankfurt.

Neuer, wanda ya lashe kofin duniya a 2014, yana da sauran damar buga wa Jamus wasan sada zumunta da Ukraine da kuma Greece cikin wata Yuni, kafin ta fara gudanar da Euro 2024 daga 14 ga watan Yuni.

Tuni kociyan ya bayyana wasu ‘yan wasa da aka karon farko da za su fara buga wa Jamus tamaula ciki har da na Stuttgart, Maximilian.

Shi kuwa dan kwallon Arsenal, Kai Havertz zai buga gaba tare da kyaftin Ilkay Gündogan da Florian Wirtz da kuma Jamal Musiala.

Haka kuma Nagelsmann ya ce Toni Kross wanda ya amince ya ci gaba da yi wa Jamus tamuala bayan ritaya, yana daga cikin masu buga karawar sada zumunta har da Jonathan Tah da kuma Antonio Rüdiger.

Leave a comment