Neuer da Kross na cikin ‘yan Germany na kwarya-kwarya

Watakila Manuel Neuer da Toni Kroos su halarci gasar cin kofin nahiyar Turai, bayan da aka bayyanasu cikin ‘yan wasan Germany na kwarya-kwarya don Euro 2024.

Kross, mai buga tsakiya, mai shekara 34 ya yi ritayar bugawa Germany tamaula a Yulin 2021, amma ya koma yi mata wasanni, bayan da ya tattauna da koci, Julian Nagelsmann.

Rabonda mai tsaron raga, Neuer, mai shekara 38, ya buga wa Germany tamaula tun 2022, wanda ya karye a lokacin zamiyar kankara, bayan gasar kofin duniya a Qatar World Cup.

Babu sunan ‘yan wasan Bayern Munich biyu, wato Leon Goretzka da Serge Gnabry, yayin da dan wasan Tottenham, Timo Werner ke jinya.

Mats Hummels da Julian Brandt wadanda ke taka rawar gani a Borussia Dortmund da ta kai wasan karshe a Champions League babu sunansu cikin ‘yan wasa 27 da aka bayyana, wadanda za su koma 26 bayan Germany ta buga wasan sada zumunta da Ukraine da Greece a cikin Yuni.

Wasu da aka gayyayat har da tsohon dan kwallon Manchester City, Ilkay Gundogan da na Arsenal, Kai Havertz da mai taka leda a Brighton, Pascal Gross.

Germany na fuskantar kalubale a gasar da ta kara a baya, wadda aka yi waje da ita a karawar cikin rukuni a gasar kofin duniya biyu baya.

Haka kuma aka fitar da ita a zagayen ‘yan 16 a Euro 2020, amma ana sa ran za ta taka rawar gani a matakin mai karbar bakunci.

Germany, wadda ta lashe kofin duniya a 2014 za ta fara wasa ranar 14 ga watan Yuni da Scotland da za su kece raini a Munich.

‘The 2014 World Cup winners begin their campaign on 14 June against Scotland in Munich.

‘Yan wasan Germany:

Masu tsaron raga: Oliver Baumann (Hoffenheim), Alex Nubel (Stuttgart), Manuel Neuer (Bayern Munich), Marc-Andre ter Stegen (Barcelona)

Masu tsaron baya: Waldemar Anton (Stuttgart), Benjamin Henrichs (RB Leipzig), Joshua Kimmich (Bayern Munich), Robin Koch (Eintracht Frankfurt), Maximilian Mittelstadt (Stuttgart), David Raum (RB Leipzig), Antonio Rudiger (Real Madrid), Nico Schlotterbeck (Borussia Dortmund), Jonathan Tah (Bayer Leverkusen)

Masu buga tsakiya: Robert Andrich (Bayer Leverkusen), Chris Fuhrich (Stuttgart), Pascal Gross (Brighton and Hove Albion), Ilkay Gundogan (Barcelona), Toni Kroos (Real Madrid), Jamal Musiala (Bayern Munich), Aleksandar Pavlovic (Bayern Munich), Leroy Sane (Bayern Munich), Florian Wirtz (Bayer Leverkusen)

Masu cin kwallaye: Maximilian Beier (Hoffenheim), Niclas Fullkrug (Borussia Dortmund), Kai Havertz (Arsenal), Thomas Muller (Bayern Munich), Deniz Undav (Stuttgart)

Leave a comment