Neuer ba zai buga wa Bayern Munich wasan Heidemheim ba

Manuel Neuer ba zai buga wa Bayern Munich wasan Bundesliga da ta je Heidemheim ranar Asabar ba, in ji Thomas Tuchel.

Tsohon kociyan Chelsea ya sanar ranar Juma’a cewar kimanin manyan ‘yan wasa biyar ne ke jinya a kungiyar.

Neuer mai shekara 38 ya fama rauni ne mako biyu da ya wuce lokacin da yake atisaye da tawagar Germany.

Wanda ya ji rauni bayan kammala gasar kofin duniya a Qatar a 2022, bai yi wa Germany wasan sada zumunta da France da kuma Netherlands ba.

Haka kuma bai yi wasan da Bayern Munich ta sha kashi a Bundesliga da ci 2-0 a hannun Borussia Dortmund, hakan ya sa kofin bana ya gagare ta, wadda take ta biyu a teburi da tazarar maki 13 tsakani da Bayern Leverkusun ta daya.

Sven Ulreich zai ci gaba da maye gurbin Neuer, wanda yake sa ran ko zai murmure ya tsare ragar Bayern Munich a Champions League da za ta fafata da Arsenal ranar Talata.

Sauran ‘yan kwallon da ba za su buga wa Bayern karawar ba ta ranar Aasabar sun hada da Kingsley Coman daLeroy Sane da Aleksandar Pavlovic da kuma Noussair Mazraoui.

Kofin Champions League ne kadai da Bayern ke fatan dauka a bana, idan ba haka za ta kammala kakar bana ba tare da kofi ba koda na shayi ne tun bayan 2012.

A karshen kakar nan Tuchel zai ajiye aikin horar da Bayern Munich kamar yadda ya sanar.

Leave a comment