Netherlands za ta je Euro 2024 da De Jong mai jinya

Tawagar Netherlands ta bayyana masu jinya Frenkie de Jong da Georginio Wijnaldum cikin ‘yan wasa 30 na kwarya-kwarya, domin Euro 2024.

Kusan wata daya dan kwallon Barcelona, De Jong na jinya, amma za a bashi dama ya nuna kansa ko zai iya buga gasar da za a fara a watan gobe a Germany.

Tun cikin watan Maris tawagar Netherlands ta gayyaci Wijnaldum, wanda yanke ke taka leda a Saudia Arabia, wanda tsohon dan wasan Liverpool da Newcastle da Paris St-Germain yanzu yana Al-Ettifaq – bayan wata tara yana jinya.

Cikin wadanda aka bayyana har da masu tsaron bayan Liverpool, Virgil van Dijk da Ryan Gravenberch da Cody Gakpo har da mai taka leda a Atletico Madrid, Memphis Depay.

Haka kuma har da mai tsaron bayan Arsenal, Jurrien Timber daga cikin wadanda za a tace su koma 26 daga nan zuwa 29 ga watan Mayu a lokacin aka sa ran koci, Ronald Koeman zai bayyana wadanda zai je da su Germany.

Tawagar Netherlands za ta fafata da Canada da Iceland a wasan sada zumunta a watan gobe daga nan ta ke Germany, domin fara wasa da Poland a Hamburg ranar 16 ga watan Yuni.

Haka kuma tawagar da Koeman ke jan ragama tana rukuni na hudu da ya hadu da France da Austria.

‘Yan wasan kwarya-kwarya da Netherlands ta bayyana domin Euro 2024

Masu tsaron raga: Justin Bijlow (Feyenoord), Mark Flekken (Brentford), Bart Verbruggen (Brighton & Hove Albion), Nick Olij (Sparta Rotterdam)

Masu tsaron baya: Nathan Ake (Manchester City), Daley Blind (Girona), Virgil van Dijk (Liverpool), Denzel Dumfries (Inter Milan), Jeremie Frimpong (Bayer Leverkusen), Lutsharel Geertruida (Feyenoord), Matthijs de Ligt (Bayern Munich), Ian Maatsen (Borussia Dortmund), Micky van de Ven (Tottenham Hotspur), Stefan de Vrij (Inter Milan)

Masu Buga tsakiya: Ryan Gravenberch (Liverpool), Frenkie de Jong (Barcelona), Teun Koopmeiners (Atalanta), Tijjani Reijnders (AC Milan), Marten de Roon (Atalanta), Jerdy Schouten (PSV Eindhoven), Xavi Simons (RB Leipzig), Quinten Timber (Feyenoord), Joey Veerman (PSV Eindhoven), Georginio Wijnaldum (Al-Ettifaq)

Masu cin kwallaye: Steven Bergwijn (Ajax), Brian Brobbey (Ajax), Memphis Depay (Atletico Madrid), Cody Gakpo (Liverpool), Donyell Malen (Borussia Dortmund), Wout Weghorst (Hoffenheim, on loan from Burnley)

Leave a comment