Netherlands da Romania da Switzerland sun samu gurbin Euro 2022

Tawagar kwallon kafa ta Netherlands da ta Romania da kuma ta Switzerland, sun samu gurbin buga Euro 2024.

Hakan ya biyo bayan nasara da suka samu a wasannin da suka buga ranar Asabar a rukunnansu.

Wout Weghorst ne ya ci kwallon a minti 12 da take leda a Amsterdam, hakan ya sa Netherlands ta yi ta biyu a rukunin farko da Faransa ta ja ragama.

Ita kuwa Romania ta yi nasarar doke Hungary da cin 2-1 a rukuni na tara, wadda aka fara zura wa kwallo daga baya ta farke ta kara.

Da wannan sakamakon Switzerland tana da tabbacin zama cikin ‘yan biyun farko a rukunin duk da tashi 1-1 da Kosovo da ta yi a Basel.

Wasannin da za a buga ranar Lahadi:

Hungary da Montenegro

Serbia da Bulgaria

Belgium da Azerbaijan    

Sweden da Estonia 

Scotland da Norway        

Spain da Georgia    

Liechtenstein da Luxembourg

Bosnia And Herzegovina da Slovakia      

Portugal da Iceland

Leave a comment