NBA ta ci tarar Brooks da Udoka kan cin mutuncin rafli

Hukumar kwallon kwandon Amurka, NBA ta ci tarar dan wasan Houston Rockets, Dillon Brooks $35,000.

Haka kuma ta ci tarar kociyan, Rockets Ime Udoka $25,000 ranar Talata bisa fadar kalaman da ba su dace ba ga alkalin wasa.

Lamarin ya faru ne a wasa da Milwauke a NBA ya rage dakika 38 a tashi, inda Rockets ta yi rashin nasara da ci 128-119 ranar Lahadi a Milwaukee.

An sayo Brooks mai shekara 27 dan kasar Canada a Yulin bana daga Memphis.

Udoka an sauke shi daga kociyan Boston Celtics bayan cacar baki da ya yi da wani ma’aikacin kungiyar, hakan ya saba ka’idar aikin.

Daga nan Rockets ta dauke shi aiki a cikin watan Afirilu.

Leave a comment