Napoli ta kori Garcia ta sake dawo da Mazzarri

Kungiyar Napoli ta sanar da korar koci, Rudi Garcia ranar Talata, bayan da ba ta taka rawar gani a gasar Serie A ta bana.

Napoli ta ce ta sake dawo da Walter Mazzarri, domin ya maye gurbin Garcia dan kasar Faransa, wanda Napoli take ta hudun teburin teburi da tazarar maki 10 tsakaninta da Inter Milan ta daya.

Bayan da aka buga wasannin mamo na 12, Inter tana ta daya da maki 31, sai Juventus mai maki 29 ta biyu da kuma AC Milan ta uku mai maki 23 a teburin Serie A na bana.

Garcia ya karbi aikin horar da Napoli daga 1 ga watan Yulin 2023, bayan da ya maye gurbin Luciano Spalleti.

A bara ne Napoli ta lashe Serie A, sannan ta kai quarter finals a Champions League.

Watter Mazzarri ya horar da Napoli daga 6 ga watan Oktoban 2009 zuwa 27 ga watan mayun 2013.

Kociyan ya lashe Coppa Italia da Supercoppa Italiana da ya yin a biyu a 2012 da kuma yin na biyu a Serie A a kakar 2012/13.

Leave a comment