Napoli ba ta yanke shawara kan daukar TRAORE BA

Har yanzu Napoli ba ta yanke shawara ko za ta dauki dan wasan Bournemouth, Hamed Traore, wanda ke yi mata wasannin aro.

Bayan da Bournemouth ta dauki aron Traore daga Sassuolo a Janairun 2023, an hada da yarjejeniyar sayar da shi kan £25m idan ya taka rawar gani.

Kungiyar da ke buga Premier League ta auna ba za ta biya kudin ba, wanda wasa biyar kacal ya buga mata da canjin ‘yan wasa karo biyu a babbar gasar tamaula ta England.

Traore ya kwan da sanin cewar koci, Andoni Iraola ba zai ke saka shi a wasannin ba sosai, hakan ya sa aka amince dan kwallon tawaagar Ivory Coast ya koma Napoli da yin wasannin aro.

Tun daga lokacin matashin mai shekara 24 ya nuna kansa karkashin kociya, Francesco Calzona, wanda aka fara wasa biyar da shi a cikin fili ya kuma canji ‘yan wasa karo biyu.

Napoli, wadda ta lashe Serie A bayan kammala kakar 2023 watakila ta yanke shawarar sayen dan kwallon kan €25m.

Leave a comment