Najeriya za ta kori Peseiro idan ta samu kudin hakkinsa

Da tuni hukumar kwallon kafar Najeriya ta sallami koci, Jose Peserro da tana da kudin biyan hakkinsa, in ji wani babban jami’in Nff, Nse Essien.

Super Eagles ta fara wasannin neman shiga gasar cin kofi duniya da kafar hagu, bayan da ta tashi 1-1 da Lesotho da kuma Zimbabwe.

Ana ta caccakar kociyan dan kasar Portugal da cewar ba zai iya kai Najeriya gasar kofin duniya ba a 2026

‘’Da a ce muna da kudin da za mu biya kociyan dukkan hakkinsa da tuni mun sallame shi, ba ma jin dadin yadda yake gudanar da aikinsa’’, in ji Essien.

‘’Ana ta kiraye-kirayen a kori kocin. Abin takaici ne daga maki shida ace biyu muka hada. Muna cikin wani hali.’’

Afirka ta Kudu ce ke jan ragamar teburin rukuni na uku da maki uku, wadda za ta kara da Rwanda a ranar Talata, sai Lesotho ta karbi bakuncin Benin.

Super Eagles wadda ta kasa samun tikitin shiga gasar 2022 a Qatar ta hada maki biyu daga wasa biyu a rukuni na uku.

Za a ci gaba da wasannin cikin rukuni a cikin watan Yuni, inda Super Eagles za ta karbi bakuncin Afirka ta Kudu a Uyo, sannan ta ziyarci Benin.

Amurka da Mexico da kuma Canada ne za su karbi bakuncin gasar kofin duniya a 2024.

Leave a comment