NagelsmanN zai maye gurbin Tuchel a Bayern Munich

Kociyan tawagar Germany, Julian Nagelsmann ne zai maye gurbin Thomas Tuchel a Bayern Munich a wani rahoto da The Bild ta wallafa a karshen mako.

Kamar yadda rahoton yake tuni mahukuntan Bayern Munich suka tattauna da matashin kociyan domin sake damka masa aikin kociyan kungiyar.

Cikin watan Maris din 2023 Bayern Munich ta kori kociyan ta maye gurbinsa da Tuchel, wanda tuni ya sanar da cewar zai ajiye aiki da zarar an kammala kakar bana.

Tun farko kociyan Bayern Leverkusen, Xavi Alonso kungiyar Bayern Munich ta yi shirin dauka, sai dai tsohon dan wasan Liverpool ya sanar ranar Juma’a cewar zai ci gaba da aiki da Leverkusen.

Kawo yanzu Nagelsmann yana da kunshin kwantiragi da tawagar Jamus zuwa karshen gasar Euro 2024, wadda za a fara daga 14 ga watan Yuni zuwa 14 ga watan Yulin bana a Germany.

Nagelsmann ya fara jan ragamar tawagar Jamus da doke USA da yin canjaras da Mexico daga baya ya yi rashin nasara a hannun Turkey da kuma Austria.

Cikin watan Maris ya ja raamar Germany ta doke France da Netherlands a wasan sada zumunta.

Leave a comment