Nadal zai koma tennis a Brisbane a Disamba

Rafael Nadal zai koma kwallon tennis a Disamba a Brisbane, bayan kusan shekara daya rabonsa da wasan.

Rabon da ya buga tennis tun raunin da ya ji a wasa da Mackenzie McDonald a Australian Open a watan Janairu.

Mai grand slam 22, wanda tun farko ya dauka gajeriyar jinya zai yi, ya sanar a cikin watan Mayu cewar ya kusan yin ritaya.

Dan kasar Spain ya kara da cewar watakila ya hakura da wasan a karshen kakar 2024.

A cikin watan Yuni aka yi masa aiki, wanda ya sanar da cewar zai koma wasa a Brisbane daga 31 ga watan Disamba, wadda ake yi kafin tunkarar Australia Open.

Nadal ya sanar da hakan a kafar sada zumuntarsa ta twitter wato X da cewar ‘’Mu hadu a Brisbane a farkon makon Janairu’’.

Mai shekara 37 yanzu yana mataki na 663 a matsayin wadanda ke kan gaba a kwallon tennis a duniya.

A watan Maris ya rasa gurbinsa karon farko daga cikin ‘yan goman farkon teburi tun bayan shekara 18.

Haka kuma a gasar ta Brisbane ana sa ran Naomi Osaka za ta koma fagen daga, bayan haihuwa da ta yi a cikin watan Yuli.

Leave a comment