Nadal ya ci wasan farko a tennis bayan jinya

Rafael Nadal ya yi nasara a karon farko a gasar kwallon tennis, bayan jinyar kusan shekara daya.

Ya doke zakaran US Open, Dominic Thiem a wasan farko a Brisbane International ranar Talata.

Wanda ke rike da Grand Slam 22, mai shekara 37 ya yi nasara da cin 7-5, 6-1 a Pat Rafter Arena.

Leave a comment