Musiala zai koma buga wa Bayern Munich wasanni

Jamal Musiala yana cikin ‘yan wasan Bayern Munich da za ta kara da Union Berlin ranar Asabar a Bundesliga.

Sai dai har yanzu matashin dan wasan bai shirya buga wasa minti 90 ba.

Musiala ya ji rauni a Nuwamba tun daga lokacin yake jinya, bai yiwa Jamus wasan sada zumunta da Turkey ba da na Austria.

Haka wasu ‘yan wasan Bayern Munich da suka murmure sun hada da Eric Maxim Choupo-Moting da Minjae Kim da kuma Noussair Mazraoui.

A wasan na ranar Asabar shi ne na farko da koci, Nenad Bjelica zai fara jan ragamar Berlin, wadda ta kori Urs Fischer.

Bayern Munich tana mataki na biyu a teburin Bundesliga da tazarar maki biyu tsakaninta da Bayern Leverkusen mai jan ragama.

Thomas Tuchel ya sanar cewar Bayern Munich za ta buga wasan sada zumunta a Basel ranar 6 ga watan Janairu, kafin a kammala hutun Kirsimeti a Bundesliga.

Leave a comment