Muller zai ci gaba da wasa a Bayern Munich zuwa 2025

Thomas Muller ya saka hannu kan karin kwantiragin shekara daya da zai kare a karshen Yunin 2025.

Tun farko yarjejeniyar dan wasan za ta kare a karshen Yunin 2024, yanzu an kara shekara daya akai.

Dan kasar Germany, mai shekara 34 ya yi gabaki dayan rayuwarsa ta tamaula a Bayern Munich, wadda ya yiwa wasa 684 tun daga lokacin da ya fara buga mata tamaula a 2008.

Muller ya lashe Bundesliga 12 da Champions League biyu da German cups shida da German Super cups takwas.

Bayern Munich mai kwantan wasa daya tana ta biyun teburin Bundesliga da tazarar maki hudu tsakaninta da Bayern Leverkusen ta daya.

Leave a comment