Muller na kwadayin ci gaba da taka leda bayan kakar nan

Dan kwallon tawagar Jamus, Thomas Muler na sa ran ci gaba da taka leda koda kwantiraginsa ya kare a karshen kakar nan.

‘’Ina matukar son ci gaba da taka leda bayan 2024, ina jin dadin rawar da nake takawa a fili, ina fatan kunga hakan.’’

Muller ya koma Bayern Munich tun yana karami a 2000 tun daga makarantar horor da tamaular kungiyar.

Ya  fara buga wa Bayern Munich wasa a cikin 2008.

Ya lashe kofi tare da Bayern Munich har da uku rigis a kakar 2013 da kuma 2020.

Ya ci kwallo 164 ya bayar da 161 aka zura a raga a wasa 470 da ya yiwa kungiyar.

Wanda ya ja ragamar Bayern a matakin Kyaftin sau 125, ya kuma lashe kofin duniya a 2014.

Dan wasan watakila ya koma taka leda a wata kungiyar a gasar Jamus.

Leave a comment