Moyes zai bar West Ham a karshen kakar nan

Kociyan West Ham United, David Moyes zai bar kungiyar a karshen kakar bana, sakamakon da ba ta kokari a bana.

West Ham ta sanar da cewar kociyan zai bar kungiyar kwana daya tsakani da Chelsea ta doke ta 5-0 ranar Lahadi a gasar Premier League a Stamford Bridge.

Kamar yadda kungiyar ta sanar ”David Moyes zai bar kungiyar a karshen kakar 2023/24 kamar yadda muka amince a tsakaninsmu.”

West Ham ta yi nasara daga daga karawa tara a Premier League, wadda ta yi kasa zuwa ta tara a babbar gasar tamaula ta Ingila, an kuma fitar da ita a Europa League zagayen daf da na kusa da na karshe.

Tuni kuma kungiyar ta sanar cewar Julian Lopetegui ne zai maye gurbin Moyes da zarar an kammala kakar nan.

Koda yake ba a kai ga cinma rattaba kwangila ba, amma tsohon kociyan tawagar Spain da Real Madrid da Wolverhampton ya maince zai kara komawa horar da tamaula a England.

Wanda ya dauki Europa League a Sevilla ya ja ragamar Wolves a lokacin da take karshen teburi daga baya ya kaita gurbin ci gaba da taka rawar gani a Premier League.

Daga baya Lopetegui ya yi murabus, bayan da ya auna tattalin arzikin ya kuma fuskanci babu kudin da za a sayo manyan ‘yan kwallo.

Leave a comment