Morocco tana da masu takarar gwarzon Afirka da yawa

Tawagar kwallon kafa ta Morocco tana da ‘ya wasa hudu daga 10 da ke takarar gwarzon dan kwallon Afirka na 2023.

‘Yan wasan sun hada da mai tsaron raga, Yassine Bounou da mai tsare baya, Achraf Hakimi da mai wasa daga tsakiya, Sofyan Amrabat da mai cin kwallaye, Youssef En-Nesyri.

A gasar kofin duniya a Qatar a 2022, Morocco ita ce ta ja ragamar rukunin da yake dauke da Belgium.

Sannan ta fitar da Sifaniya da kuma Portugal, kafin tayi rashin nasara a hannun Faransa a daf da karshe.

Ta kafa tarihin tawagar tamaula daga Afirka da ta kai zagayen daf da karshe a karon farko a gasar kofin duniya.

Sauran da ke cikin ‘yan takara har da wadanda suka lashe kyautar karo biyu wato Mohamed Salah na Masar da Sadio Mane na Senegal.

Haka kuma har da Riyad Mahrez na Algeria, wanda ya taba lashe kyautar, yanzu yana taka leda a gasar Saudi Arabia.

‘Yan wasan Kamaru biyu Andre-Frank Zambo Anguissa da Vincent Aboubacar da na tawagar Najeriya, Victor Osimhen suke cike sauran gurbin.

Za a sanar da gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na 2023 a wani biki da za a gudanar a Morocco a birnin Marrakesh ranar 11 ga watan Disamba.

Leave a comment