Morant zai koma NBA bayan dakatarwa wasa 25

Fitatcen dan wasan kwallon kwandon Amurka, NBA Ja Morant ya ce ya ji takaici da baya buga wasanni, sakamakon hukunta shi da aka yi.

Dan wasan, wanda ya kammala hukuncin dakatarwa wasa 25 na shirin komawa buga wa Memphis Grizzlies kwallon Kwando.

Morant ya motsa jiki ranar Juma’a, wanda aka hukunta, bayan wani bidiyo biyu a kafar sada zumunta da yake dauke da bindiga.

Dan wasan dan kasar Amurka mai shekara 24, wanda aka zaba a matakin mai tasowa da ba kamarsa a 2022, zai iya komawa wasa ranar Tatala a karawa tsakanin Grizzlies da New Orleans.

An dakatar da Morant wasa takwas a cikin watan Maris, bayan wani bidiyo da yake dauke da bindiga a gidan rawa a Denver.

A cikin watan Mayu aka kara ganin Morant a wani bidiyo dauke da bindiga, dalilin da aka dakatar da shi wasa 25 kenan.

Leave a comment