Modric bai yanke makomarsa a Real Madrid ba

Wasu rahotanni na cewar Luka Modric bai fayyace makomarsa ba a Real Madrid ba, duk cewar nan da wata biyu kwantiraginsa zai kare a Santiago Bernabeu.

Dan kasar Crotia an tursasa masa ya amince an rage masa rawar da yake takawa a kungiyar a kakr 2023/24 ciki har da zaman benci da ba a fara wasa da dan kwallon mai shekara 38.

Sai dai har yanzu Modric na buga wa Real tamaula, wanda aka fara wasa 36 a dukkan karawa a bana har da wanda kungiyar Santiago Bernabeu ta je ta ci Real Mallorca 1-0 a gasar La Liga ranar Asabar.

Modric ya fara da zaman benci a karawa da Manchester City a Spain a Champions League a wasan farko a daf da na kusa da na karshe ranar Talata.

Ana sa ran dan kasar Croatia zan kara zaman benci a wasa na biyu da Manchester City ranar Laraba a Etihad, duk da cewar Aurelien Tchouameni na hutun dakatarwa.

Aana sa ran Eduardo Camavinga da Toni Kroos da kuma Federico Valverde ne za su buga gurbin tsakiya a Real Madrid a wasa na biyu a Etihad.

Jude Bellingham ake sa ran za su buga gaba tare da Vinicius Junior da Rodrygo, bayan da Real ke fatan kai wa zagayen daf da karshe, bayan tashi 3-3 a wasan farko a Spain.

Manchester City ce ta fitar da Real Madrid a Champions League ta ta je ta lashe kofin a karon farko a tarihi.

Leave a comment