MLS 2024: Inter Miami za ta fara wasa da Real Salt Lake a Fabrairu

Kungiyar Lionel Messi, Inter Miami za ta fara wasan farko da Real Salt Lake a gasar kwallon kafar Amurka ta badi.

Za ta fara da karbar bakuncin wasan farko ranar 21 ga watan Fabrairu a Major League Soccer.

Gasar ita ce ta 29 da za a gudanar a 2024, inda kyaftin din Argentina zai fara wasa tun daga farko a kungiyar da ke Florida.

Ana tsada da gasar MLS Messi ya koma Amurka da taka leda, bayan da yarjejeniyarsa ya kare a Paris St Germain.

Messi zai buga wasa na biyu da Inter Miami da za ta je gidan Los Angeles Galaxy ranar 25 ga watan Fabrairu.

Kowacce kungiya za ta buga wasa 34 a badi, guda 17 a gida da wasu 17 a waje, inda ake sa ran Inter Miami za ta samu karin magoya bayan zuwa kallon Messi.

Inter Miami za ta buga wasan karshe a gida ranar 19 ga watan Oktoba a wasan da za ta yi da New England.

Za a buga wasan karshe a kofin MLS na 2024 ranar 7 ga watan Disamba.

Messi ya ja ragamar Inter Miami ta lashe League Cup a bara, kofin farko da kungiyar ta dauka.

Za a buga kofin bana tsakanin 26 ga watan Yuli zuwa 25 ga watan Agustan 2024 tsakanin kungiyoyin MLS da na Mexico.

Leave a comment