Militao ya buga wa Real Madrid wasa na 150

Ranar Laraba Real Madrid ta doke Bayern Munich ta kuma kai wasan karshe a Champions League na bana.

Eder Militao ya buga karawar, kuma ita ce ta 150 da mai tsaron bayan ya buga a kaka ta biyar da cin kwallo 11 da lashe kofi 11 a kungiyar.

Cikin karawa 150 an ci wasa 98 da shi a fili, wanda ya buga wasa 102 a La Liga da 32 a Champions League da wasa 11 a Copa del Rey da hudu a Spanish Super Cup da daya a European Super Cup.

Kakar da Militao ya buga wasa da yawa ita ce wadda ya yi 51 a dukkan fafatawa, sai dai dan kwallon Brazil ya buga wasa takwas ne a bana, bayan da ya sha jinya ta wata takwas.

Real Madrid, wadda ta lashe La Liga na bana na 36 jimilla za ta buga wasan karshe a Champions League da Borussia Dortmund, wadda ta fitar da Paris St Germain.

Za a buga wasan karshen ranar 1 ga watan Yuni a Wembley.

Leave a comment