Messi da Haaland da Mbappe na takarar gwarzon Fifa na 2023

Lionel Messi da Erling Haaland da Kylian Mbappe, sune ukun da suka rage da ke takarar gwarzon dan kwallon Fifa na 2023.

Messi, wanda ya lashe kyautar fitatcen dan kwallon kafa a 2022, ya ja ragamar Argentina ta lashe kofin duniya a Qatar a karon farko tun bayan 1986, kuma na uku jimilla.

Argentina ta yi nasarar doke France a wasan karshe a bugun fenariti a lokacin da su Mbappe ke rike da kofin da suka lashe a Russia a 2018.

Shi kuwa Haaland ya taimakawa Manchester City ta lashe kofi uku a karon farko da ta dauki UEFA Champions League da Premier League da kuma FA Cup.

Mbappe, wanda ke ta fafutukar yadda zai koma taka leda a Real Madrid, ya ja ragamar Paris St Germain ta lashe Ligue 1, kuma shi ne kan gaba a cin kwallaye, wanda ya kai wasan karshe a gasar kofin duniya a Qatar a 2022.

Masu takara a fannin mata kuwa sun hada da ‘yan Spain, Aitana Bonmati da Jennifer Hermoso da kuma ta Colombia Linda Caicedo.

Ranar 15 ga watan Janairun 2024 za a bayyana gwarzon dan kwallon Fifa na 2023 a bikin da za a gudanar a London.

Leave a comment