Me kuke son sani kan wasan Arsenal da Luton?

Arsenal za ta karbi bakuncin Luton Tiwn ranar Laraba a wasan mako na 32 a Premier League a Emirates.

Sun kara a wasan farko a bana ranar 5 ga watan Disambar 2023, inda Gunners ta je ta ci 4-3.

Arsenal mai kwantan wasa tana ta biyun teburin Premier da tazarar maki daya tsakaninta da Liverpool ta daya, ita kuwa Luton mai maki 22 tana ta ukun karshen teburi, wato ta 18.

Kocin Arsenal, Mikel Arteta ya ce Bukayo Saka na cikin koshin lafiya, duk da ba a kammala wasan Manchester City da shi a cikin fili ba.

Wanda kawai ke jinya a Arsenal shi ne Jurrien Timber, wanda ake sa ran sai bayan kammala kakar bana zai murmure.

Shi kuwa kociyan Luton, Rob Edwards ya ce bai da tabbaci ko Alfie Doughty da Reece Burke da kuma Tahith Chong ko za su iya buga masa fafatawar.

Kimanin ‘yan wasa 10 ke jinya daga kungiyar Luton Town.

Wasu batun da ya kamata ku sani

  • Arsenal na fatan doke Luton gida da waje a bana karon farko tun bayan 1983-84.
  • Luton ta yi rashin nasara 10 a fafatawar da ta ziyarci Gunners, sai dai rabon da su fuskanci juna tun Agustan 1991 a Highbury.

Arsenal

  • Arsenal ta yi nasara tara daga wasa 10 baya a Premier League a Emirates da cin kwallo 14 aka zura mata uku a raga.
  • Kwallo hudu ne ya shiga ragar Arsenal a wasa tara a lik a shekarar 2024.
  • Gunners ta lashe wasa biyar a lik da ta fuskanci sabbin kungiyoyin da suka hau Premier League.
  • Cikin wasa 38 da Arsenal ta buga a gida da sabbin kungiyar da ta hau Premier League ta ci 33 da canjaras biyar.

Luton Town

  • Luton ta zura kwallo a raga a wasa 18 baya a Premier League ita ce kan gaba a wannan bajintar a bana.
  • Sai dai wasa hudu ta ci daga karawa 18 sannan ba ta yi nasara ba a karawa tara baya, mai canjaras uku da rashin nasara shida.
  • Maki hudu Luton ta hada daga 24 da ya kamata ta samu a Premier League a wasan dare.
  • Wasa daya Luton ta ci a karawa 40 da ta je London shi ne wanda ta doke Wimbledon a Plough Lane cikin Fabrairun1990,

Leave a comment