Mbappe ya sanar zai bar PSG a karshen kakar nan

Dan kwallon tawagar France, Kylian Mbappe ya sanar da cewar zai bar Paris St-Germain a karshen kakar nan.

Mbappe, mai shekara 25, ya sanar da hakan a wani bidiyon da ya saka a kafarsa ta sada zumunta.

Kwantiragin Mbappe a PSG zai kare a karshen kakar watan Yuni, kuma tun cikin watan Fabrairu aka bayar da rahoton cewar dan kwallon ya amince zai koma Real Madrid da taka leda a badi.

Wanda ya lashe kofin duniya, shi ne kan gaba a ci wa PSG kwallaye a tarihi mai 255 a raga, zai buga wa kungiyar wasan karshe a karawa da Toulouse a Ligue 1 ranar Lahadi.

Bayan nan PSG tana da wasa a gidan Nice ranar 15 ga watan Mayu da Nice da fafatawa da Metz ranar 19 ga watan da kuma French Cup da Lyon a Stade Pierre-Mauroy a Lille ranar 25 ga watan Mayu.

Mbappe, wanda aka haifa a birnin Paris, ya koma PSG daga Monaco a Agustan 2017 kan £165.7m.

Leave a comment