Tawagar France national football team ta doke ta Brazil national football team da ci 2-1 a wasan sada zumunta, domin shirin tunkarar FIFA World Cup da za a yi a Amurka, Canada da Mexico.
Kylian Mbappé ne ya fara jefa ƙwallo a minti na 32 a wasan da aka buga a filin Gillette Stadium.
Wannan ita ce ƙwallo ta 56 da Mbappé ya ci wa Faransa a wasa 95, inda yanzu ya rage masa guda ɗaya kacal ya kai yawan ƙwallayen Olivier Giroud mai 57 a raga a wasa 137.
Daga baya, Hugo Ekitike ya ci wa Faransa ƙwallo ta biyu, kafin Brazil national football team ta zare ɗaya hannun Bremer.
An sauya Mbappé a minti na 66, inda Marcus Thuram ya maye gurbinsa domin ya samu hutu, bayan dawowa daga jinya da ya yi a Real Madrid.
Sai dai Faransa ta kammala wasan da ƴan ƙwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Dayot Upamecano jan kati sakamakon keta da ya yi wa Wesley.
A bangaren Brazil kuwa, tawagar karkashin jagorancin Carlo Ancelotti ta buga wasan ba tare da Neymar ba, wanda shi ne kan gaba a yawan ci wa ƙasar ƙwallaye.
Jerin ƴan wasan da ke kan gaba a cin ƙwallaye a tawagar France:
Dan wasa Ƙwallaye Yawan wasa Kakar wasa
| Olivier Giroud | 57 | 137 | 2011-2024 |
| Kylian Mbappe | 56 | 94 | 2017-har zuwa yanzu |
| Thierry Henry | 51 | 123 | 1997-2010 |
| Antoine Griezmann | 44 | 137 | 2014-2024 |
| Michel Platini | 41 | 72 | 1976-1987 |
| Karim Benzema | 37 | 97 | 2007-2022 |
| David Trezeguet | 34 | 71 | 1998-2008 |
| Zinedine Zidane | 31 | 106 | 1994-2006 |
