Manchester United za ta dauki mai cin kwallaye bayan kakar nan

Kociyan Manchester United, Erik Ten Hag ya ce zai sayo mai cin kwallaye da zarar an kammala kakar bama.

Tun farko kociyan dan kasar Netherlands ya ce masu buga masa gurbin cin kwallaye sun wadatar da kungiyar.

To amma da yake saura wasa bakwai a kammala Premier League ta kakar nan, kwallo 45 ta zura a raga, ita ce mai karaci daga cikin goman farkon teburi.

United, wadda ta je gidan Bournemouth buga Premier League ranar Asabar ta dauki dan kasar Denmark, Rasmus Hojlund daga Aatalanta cikin Agusta kan yarjejeniyar kaka biyar kan £72m.

Mai shekara 21 shi ne kan gaba a yawan ci wa United kwallaye mai 13 a raga a fafatawa 34 a dukkan karawa.

Shi kuwa dan wasan tawagar England, Marcus Rashford ya ci takwas a karawa 38, dan wasan tawagar France kuwa Aanthony Martial mai yawan jinya ya ci kwallo biyu a wasa 19.

a

Leave a comment