Man City ta yi wasa na 42 a gida a jere ba a doke ta ba

Manchester City ta buga wasa na 28 a dukkan karawa ba tare da an doke ta ba a dukkan fafatawa, bayan da ta tashi 1-1 da Real Madrid a Etihad.

Real Madrid ta kai zagayen daf da karshe a Champions League, bayan da ta yi nasara a kan City da cin 4-3 a bugun fenariti, bayan karin lokaci, wadanda suka tashi 3-3 a wasan farko a Santiago Bernabeu.

Haka kuma wasa na 42 kenan da City ta buga a gida ba tare da rashin nasara ba, rabonda a doke ta tun bayan Nuwambar 2022, inda Brentford ta ci 2-1 a Etihad a Premier League.

Manchester City, wadda ta dauki kofi uku a bara ta yi fatan maimaita hakan, amma yanzu Champions League ya kubuce mata, saura biyu kenan da take fatan lashewa a bana.

A bara ne City ta dauki Champions League da FA Cup da kuma Premier League, karon farko da ta ci kofin zakarun Turai da kuma uku rigis a kaka daya.

Ranar Asabar City za ta kara da Chelsea a Wembley, kofin da ta lashe a bara, daya daf da karshe za a yi ne tsakanin Coventry City da Manchester United.

Manchester City tana ta daya a kan teburin Premier League da maki 73 da tazarar maki biyu tsakani da Arsenal da Liverpool da kowacce keda 71, saura wasa shida su karkare kakar bana.

Leave a comment