Man City ta koma ta hudun teburin Premier

Aston Villa ta yi nasara a kan Manchester City da cin 1-0 a Villa Park a wasan mako na 15 a Premier League.

Leon Bailey ne ya ci wa Villa kwallon, saura minti 16 a tashi daga karawar ta Villa Park.

Aston Villa ta yi nasara a wasa 10 daga 15 da ta fafata a Premier League a bana, kwazo mai kyau tun bayan 1980/81 da ta dauki kofin.

Da wannan sakamakon Aston Villa ta kwace mataki na uku ta yi kasa da Manchester City zuwa ta hudu.

Kungiyar da Pep Guardiola ke jan ragama tana da tazarar maki shida tsakaninta da Arsenal ta daya.

Wannan shi ne wasa mafi muni da Man City ta buga mai rike da Premier League.

Ta kuma ci karo da koma baya ne, bayan wasa hudu ba tare da yin nasara ba.

Kungiyar Etihad ta yi canjaras da Chelsea da Liverpool da kuma Tottenham, yanzu ta yi rashin nasara a Villa Park.

Man City na kara fuskantar kalubale, bayan da za ta buga wasa da yawa a cikin Disamba, ciki har da Fifa World Club Cup a Saudi Arabia.

Leave a comment