Man City ta kai wasan karshe a FA Cup

Manchester City ta kai wasan karshe a FA Cup, bayan da ta yi nasara a kan Chelsea da ci 1-0 ranar Asabar a Wembley.

Wannan shi ne karo na uku da za su fafata a bana, bayan da suka fara tashi 4-4 a Premier League cikin Nuwamba a Stamford Bridge, sannan suka yi 1-1 a Etihad cikin Fabrairu a babbar gasar tamaula ta England.

2023/2024

FA Cup Asabar 20 ga watan Afirilu

Man City         1 – 0     Chelsea 

Premier League Asabar 17 ga watan Fabrairu     

  • Man City         1 – 1     Chelsea          

Premier League Lahadi 12 ga watan Nuwamba              

  • Chelsea           4 – 4     Man City

Sai dai wannan shi ne karo na tara da suka kece raini a FA Cup, yayin da Manchester City mai rike da na bara ta ci wasa shida, Chelsea ta yi nasara uku ba canjaras a tsakaninsu.

Tun farko Manchester City ta sa ran lashe kofi uku a bana kamar yadda ta yi a bara ta dauki Premier League da FA Cup da kuma Champions League, amma Real Madrid ta fitar da ita a gasar bana a Etihad a bugun fenariti.

City ta koma ta biyu a kan teburin Premier League da maki 73, yayin da Arsenal ta koma ta daya ranar Asabar, bayan doke Wolverhampton 2-0 a Molineux, Liverpool mai maki 71 ne da ita wadda za ta fafata da Fulham ranar Lahadi a Craven Cottage.

Chelsea tana mataki na tara a teburin Premier League da maki 47, za ta kare kakar bana ba tare da daukar kofi ba, bayan da Liverpool ta yi nasara a kanta a Carabao Cup a wasan karshe a Wembley a kakar nan.

Kenan City tana sa ran lashe FA Cup da Premier League a kakar nan, yayin da Chelsea wadda karo na biyu a jere da ba za ta je gasar zakarun Turai ba ke fatan daukar FA Cup.

Kungiyar Stamford Bridge tana da FA Cup takwas jimilla, yayin da wadda take Etihad tana da bakwai.

Daya wasan daf da karshe za a buga ne tsakanin Coventry City da Manchester United a Wembley ranar Lahadi.

Leave a comment