Man City ce za ta dauki Premier na bana – Guardiola

Pep Guardiola ya ce Manchester City ce za ta lashe Premier League na bana kuma na hudu a jere.

Kociyan ya kara da cewar duk da canjaras uku da ya yi a jere da Chelsea da Liverpool da kuma Tottenham, har yanzu sune za su lashe kofin.

Haka kuma Man City tana mataki na uku a teburin Premier League da tazarar maki uku tsakaninta da Arsenal ta daya.

Ranar Talata, Arsenal za ta je gidan Luton Town a wasan mako na 15, yayin da Man City da Aston Villa za su kara ranar Laraba.

Man City tana fama da Baraka a baya, wadda aka zurawa kwallo takwas a wasa uku baya.

Za kuma ta je Villa Park don fuskantar Unai Emery, wanda ya ci wasa 13 baya a gida.

Man City za ta buga wasan ba tare da Rodri ba, wanda aka dakatar – an doke City wasa uku duk lokacin da aka dakatar da dan kwallon.

John Stone ya murmure, watakila Guardiola ya saka dan kwallon a gurbin tsakiya, kamar yadda ya sanar.

A bara ne Man City ta dauki Premier League da FA Cup da kuma Champions League.

Leave a comment