Maguire zai yi jinyar mako uku

Manchester United ta sanar cewar mai tsaron bayan tawagar England, Harry Maguire zai yi jinyar mako uku.

Maguire ya bi sawun ‘yan wasan United da dama dake jinya, wanda ya ji rauni a wajen atisaye.

Kenan ba zai buga wasan Premier ba da United za ta je Crystal Palace ba ranar Litinin, sannan ba zai yi saura wasa uku da za su rage wa kungiyar da za ta yi da Arsenal da Newcastle da kuma Brighton.

Sai dai babu fargaba kan ko Maguire zai iya buga wa England gasar cin kofin nahiyar Turai, wadda sai a ranar 14 ga watan Yuni za a fara, kenan zai murmure kafin lokacin.

Watakila mai tsaron bayan zai warke kafin wasan karshe a FA Cup a Wembley da Manchester City ranar 25 ga watan Mayu.

Rashin Maguire koma baya ne da Erik Ten Hag, wanda ya hada shi a tsare baya tare da Casemiro a makon da ya wuce da United ta tashi 1-1 da Burnley a Premier League.

To sai dai Ten Hag ya ce watakila Johnny Evans ya buga wasan da za su yi da Palace ranar Litinin, amma dai Victor Lindelof da Lisandro Martinez da Raphael Varane na jinya.

United ta yi kasa zuwa mataki na takwas a teburin Premier League, bayan da Newcastle da Chelsea suka yi nasara a wasanninsu, kenan kungiyar Old Trafford ya zama wajibi ta hada maki uku a Selhurst Park ranar Litinin.

Leave a comment