Maguire ya lashe gwarzon Premier na Nuwamba

Dan wasan Manchester United, Harry Maguire ya zama gwarzon dan kwallon Premier League na watan Nuwamba.

Kenan ya zama mai tsaron baya na 15 a babbar gasar tamaula ta Ingila da ya lashe kyautar.

Maguire ya ci kyautar bayan da ya koma kan ganiya har ta kai Erik ten Hag ke saka shi a kowanne wasa.

Ya buga wa Man United dukkan karawar da ta yi a cikin watan Nuwamba, wadda ta ci wasa uku ba tare da kwallo ya shiga ragarta ba.

Maguire ya tare kwallo da ake buga wa Man United zuwa raga sau biyar, kuma shi ne na biyar a jerin wadanda ke kan gaba a cire kwallo daga hadari, sannan ya kware wajen cin kasuwar sama.

Dan kwallon tawagar Ingila shi ne mai tsaron baya na farko da ya lashe kyautar tun bayan dan wasan Liverpool, Joel Matip a Fabrairun 2022.

Shi ne kuma na uku a Man United da ya karbi kyautar bayan Nemanja Vidic da kuma Rio Ferdinand.

Maguire ya lashe kyautar daga ‘yan wasa shida da suka yi takara a yanar gizo a EA SPORTS da kuma wasu kwararru da suka fitar da zaraka.

Tun kan fara kakar na Man United ta amince da tayin da West Ham United ta yin a sayen dan kwallon, amma sai Maguire bai amince ya bar Old Trafford ba.

Wadanda suka lashe kyautar a 2023/24:

  • Watan Agusta: James Maddison
  • Watan Satumba: Son Heung-min
  • Watan Oktoba: Mohamed Salah

Leave a comment