Lyon ta nada Sage kociyan rikon kwarya

Lyon ta kori kociyanta, Fabio Grosso, bayan wata bakwai yana horar da kungiyar.

Mai shekara 46 ya kai Lyon matakin karshe a teburin bana, wanda ya ci wasa daya daga bakwai a lik.

An koreshi bayan mako 11 da ya maye gurbin Laurent Blanc a cikin watan Satumba.

Ranar Lahadi Lille ta yi nasara a kan Lyon da ci 2-0, hakan ya sa kungiyaar ta ci gaba da zama da maki bakwai, bayan wasa 12.

Grosso, dan kasar Italiya tsohon dan wasan Lyon tsakanin 2007 zuwa 2009 ya ji rauni a wani harin da aka kai wa motar ‘yan wasa a Marseille a cikin watan Oktoba.

Tun farko sai a karshen kakar 2024 ya kamata kwantiraginsa ya kare a Lyon din.

Leave a comment